Labarai
Gwamna Abba Kabir ya yi sabbin naɗi a hukumar Alhazai
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya naɗa sabon shugaban hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar da mambobinsa.
Sabon gwamnan wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya nada Alhaji Yusuf Lawan a matsayin shugaban hukumar da kuma Alhaji Rabi’u a matsayin sakataren hukumar da kuma sheikh Abbas Abubakar Daneji a matsayin mamba.
Sauran mambobin sun haɗa da Sheikh Shehi Shehi Maihula, ambasada Munir Lawan mamba sheikh Mangu maba, Hajia Aishatu Munir Matawalle mamba, Dr. Sani Mamba.
Gwamnan ya kuma bada umarnin su fara aiki nan ta ke domin tabbatar da ingantaccen aikin hajji a bana.
