Labarai
Rusau: Gwamnan Kano Ya Umarci CP Na Kano Da Ya Kamo Masu Kwasar Ganima
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana takaicinta kan yadda wasu bata gari ke kokarin lalata kadarorin jama’a da sunan kwashe baraguzan gine-gine da gwamnatin jihar ta ruguje.
Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya gaggauta kamo masu aikata irin wannan aika-aikar tare da tabbatar da cewa sun fuskanci fushin doka.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu, su kasance masu bin doka da oda tare da kai rahoton irin wadannan baragurbin barayin ga jami’an tsaro mafi kusa domin daukar matakin da ya dace.
Cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, yace, Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar jajircewar gwamnatinsa na kwato dukiyoyin al’umma da aka mallaka ba bisa ka’ida ba tare da dora jihar kan turbar da ta dace don samun gagarumar nasara.
