Labarai
Da Ɗumi-dumi: Tinubu ya dakatar da Emefiele daga shugabancin CBN
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Mista Godwin Emefiele daga muƙaminsa na gwamnan babban bankin CBN.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar a daren yau Juma’a.
Sanarwar ta ruwaito cewa, “Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, CFR daga muƙamin shugaban babban bankin nan take.”
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaba Tinubu da Mista Emefiele suka kammala wata ganawa da yammacin yau.
