Labarai
Kano: Ƴan sanda sun sake kame mutane 57 da ke fasa shaguna da sunan Ganima
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar sake kame mutane 57 da ake zargin suna fasa shaguna da sunan kwasar Ganima.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata da jami’in ta na hulɗa da jama’a SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar yau Juma’a.
Sanarwar ta ce, rundunar ta cafke mutanen ne ɗauke da wasu daga cikin irin waɗannan kayayyaki da suka ɗebo a a wuraren da gwamnatin Kano ke rushewa da aka yi gini a filaye ba bisa ƙa’ida ba.
Haka kuma, rundunar ta ce, bayan wadannan matasa da ta sake cafkewa, ta gurfanar da kimanin matasa 49 a gaban kotunan majistiri da ke Normal Sland kan zargin hada kai, sata da kuma Balla shagunan mutane.
Haka kuma rundunar ta sake gurfanarda mutane 57 a gaban kotunan na majistiri da makamancin laifukan da ake zargin matasan da aikatawa dauke da abunda suke karya shagunan jama’a, wanda a yanzu yawansu ya kai mutane dari da shida.
