Labarai
Ranar Dimokuradiyya: Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Najeriya Jawabi Na Farko A Gobe
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai gabatar da jawabinsa na farko ga ‘yan Najeriya da misalin karfe 7 na safe a ranar Litinin don tunawa da ranar dimokuradiyya ta bana.
Wata sanarwa da darektan yada labarai na fadar gwamnatin Shugaban kasa Abiodun Oladunjoye, ya fitar a yammacin ranar Lahadi, ta ce za a watsa jawaban shugaban kasa a gidan talabijin na Najeriya (NTA) da kuma gidan rediyon Najeriya.
Sanarwar ta shawarci daukacin kafafen yada labarai da sauran kafafen yada labarai da su hada kai da NTA, na gidajen talabijin da kuma Rediyon Najeriya don yada samun bayanan.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yiwa wa al’ummar kasa jawabi a ranar Litinin 12 ga watan Yuni, 2023 da karfe 7 na safe domin tunawa da ranar dimokuradiyya ta wannan shekara.
Sanarwar ta kara da cewa, “An umurci gidan talabijin, gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su hada kai da hukumar gidan talabijin ta Najeriya da gidan rediyon Najeriya domin samun bayanan,” in ji sanarwar.
