Ilimi
Da ɗumi-dumi: Gwamnatin Tinubu ta sanar da ranar fara bai wa ɗalibai bashin kuɗi
Gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta sanar da watannin Satumba da Oktoban bana a matsayin lokacin fara bai wa ɗalibai bashin kuɗi domin yin karatu.
Babban Sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya David Adejo, ne ya sanar da hakan yau Laraba yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a birnin tarayya Abuja.
A baya-bayan nan ne shugaba Tinubu, ya sanya hannu kan ƙudurin bai wa ɗaliban Najeriya bashi marar kuɗin ruwa domin samun damar gudanar da karatunsu.
