Labarai
Rundunar Yan Sanda A Kano Ta Gargadi Jami’anta Masu Karbar Cin Hanci
Rundunar ‘yan sandan Kano ta ja kunnen jami’anta, wadanda ke karbar na goro a hannun jama’a akan su kuka da kansu.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano CP Usaini Gumel ne ya yi jan kunnen lokacin da yake holen masu laifi da aka kama a wurare daban daban a jihar.
Ya ce ko kadan ba za su saurawa duk wani jami’in dan sanda da aka samu da karbar cin hanci a hannun jama’a ba.
Kwamishinan ya ce kawo yanzu an samu raguwar kwacen waya a Kano, inda ya ce a yanzu kowanne mutum na da ikon sakata ya wala ba tare da wata fargaba.
Kwamishinan ya ce wannan nasara ba za ta sa su koma suyi bacci ba, za su ci gaba da bayar da himma har sai an kawo karshen matsalar baki daya.
A cewarsa burin rundunar su shine kullum jama’a su kasance masu zama cikin kwanciyar hankali, yayin da su kuma suka himmata wajen tabbatar da tsaron rayuwa ka da duniyoyin al’umma.
