Connect with us

Labarai

Wata Kotu A Kano Ta Yankewa Wani Matashi Hukuncin Watanni A Gidan Yari

Wata kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Garin Kiru da ke Kano, ta yanke wa wani mutum mai suna Zaharaddin Sani Maidoki mazaunin jihar Kaduna, hukunci ɗaurin watanni 15 a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya.

Yanke masa hukuncin na zuwa ne, sakamakon samun sa da aikata laifin sojan gonar cewar shi lauya ne.

Mai gabatar da kara ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda ya amsa laifin sa, ba tare da ya wahalar da shari’ar ba.

Alkalin kotun mai shari’a Mallam Abdulmuminu Nuhu Gwarzo ya ya kafa masa shaidun jin ikirari kan laifin daya amsa, inda kotun ta yi amfani da dokokin shari’a ta jihar Kano karkashin sashi na 337 na shekarar 2000.

Kotun ta same shi da aikata laifin sojan gonar cewar shi lauya ne, wanda daga bisa ya bayyana cewa shi dan Jarida ne a jihar Kaduna.

Idan ba a manta ba shafin oddity24 ya ruwaito cewa, kotun ta aike da takaddar gayyata ga kungiyar lauyoyi ta jihar Kaduna kuma sun bayyana wa kotun cewar ba lauya ba ne kuma baya cikin kungiyarsu.

Tunda farko ya bayyana kansa a matsayin lauyan da zai kare wasu mutane da ake zargi da aikata wani laifi.

Mai shari’a Mallam Abdulmuminu Nuhu Gwarzo ya yanke masa hukunci n daurin shekara daya babu zabin biyan tara ba, kuma zai biya naira dubu ashirin ( 20,000) idan ya gaza biya zai shafe watanni uku a gidan ajiyar.

Kotun ta kwace littafinsa na rubuce-rubuce da katin shaidar aiki wato ID Card.

Mai shari’ar ya ce idan bai gamsu da hukuncin ba yana damar daukaka kara cikin kwanaki 30.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet