Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Samarwa Mutane Miliyan Guda Aiki

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan yi miliyan daya a duniyar yanar gizo.

Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Jamhuriyar Koriya karkashin jagorancin wakilin ta musamman ga shugaban kasar, H.E. Jang Sungmin, a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya kuma jaddada aniyar Najeriya na karfafa alaka da kasar Koriya ta Kudu, musamman wajen inganta harkokin kasuwanci, da musayar fasahohi da kuma wanzar da zaman lafiya a duniya.

Sen. Shettima ya ce “Muna shirye mu yi hadin gwiwa da ku a fannin fasaha domin nan da shekarar 2030, za a samu gibin basira da kashi 65% a duniya, inda kasashen Amurka, Rasha da Brazil ke fama da gibin basira miliyan shida. Na yi imanin Nijeriya tana cikin wani matsayi na musamman don cike wannan gibin basira saboda tamu kasa ce ta matasa.

“Kashi 75 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su cika shekara 35 ba, don haka muna neman hadin kan ku da goyon bayan horar da matasanmu kan fasahar zamani. Muna son ƙirƙirar ayyuka miliyan 1 a cikin duniyar yanar gizo. Indiya ta sami dala biliyan 120 a bara daga fitar da kayayyaki na duniya kuma muna cikin matsayi na musamman don cin gajiyar damar a fannin. Muna buƙatar kwarewar da muke gabatarwa, muna buƙatar fasaha don fitar da tsari da naku fasaha ce da za mu iya rungumi. ”

Mataimakin shugaban kasar a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa Olusola Abiola ya fitar, ya tabbatar wa gwamnatin kasar Koriya ta kudu kudurin gwamnatin Tinubu na yin hadin gwiwa da kasar Koriya don karfafa alaka da kasashen biyu, musamman daidaita gibin cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Ya kuma tabbatar wa tawagar Koriyar cewa shugaba Tinubu zai mutunta goron gayyatar takwaransa na Koriyar zuwa taron Afirka da Koriya a 2024.

Ya kara da cewa, “Ku tabbata cewa Najeriya na matukar godiya ga goyon bayan da kasar Koriya ta Arewa ke baiwa Najeriya a cibiyoyi da dama, a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, a kokarinmu na samun kujera a kwamitin sulhu da sauran hukumomin MDD.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet