Addini
Abubuwa Shida Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Babbar Sallah
A irin wannan rana ne al’ummar musulmi a fadin duniya suke gudanar da bukukuwan sallar Idi, daya daga cikin muhimman bukukuwan Musulunci guda biyu a cikin kowace shekara.
Kalandar Musulunci ta ƙunshi Idi guda biyu: Eid-ul-Fitr, bayan kammala azumin watan Ramadan, da kuma Idin Al-Adha, wanda ya yi daidai da lokacin aikin Hajji.
Eid-el-Adha shine lokacin mafi tsarki na shekara ga musulmi domin ita ce ranar aikin Hajji.
Aikin Hajji aiki ne na addini wanda dukkan musulmi ya kamata ya yi akalla sau daya a rayuwarsa. Miliyoyin Musulmai ne ke tafiya Makka kowace shekara domin aikin Hajjin.
Ga wasu bayanai da ya kamata ku sani game da Eid-ul-Adha:
1. Eid-el-Adha biki ne na Musulunci da ke tunawa da sadaukarwa da biyayyar Annabi Ibrahim ga Allah Madaukakin Sarki. Musamman, aiwatar da mafarki da Ibrahim ya yi na sadaukar da dansa Ismail lokacin da Allah ya umarce shi da ya yanka shi.
Duk da haka, kafin Annabi Ibrahim ya yi hakan, Allah ya ba shi ragon da zai yi hadaya a madadin Ismail.
2. Ranar Eid-ul-Adha an tsara ta ne bisa kalandar watan Musulunci, don haka ta bambanta kowace shekara tare da kalandar miladiyya. Sai dai kuma a kodayaushe tana zuwa ne a ranar 10 ga watan Zu al-Hijja, wato watan karshe na kalandar Musulunci. Bikin an yinaa tsahon kwana hudu.
3. Sallar Idi ita ce sallolin raka’a biyu masu muhimmanci da suke farawa ranar farko ta idi.
4. Masu iko su yi hadaya da dabbobi, sau da yawa raguna ko saniya.
5. Ana raba naman kashi uku: kashi guda na iyali, kashi daya na dangi, sai na kashi na karshe abokai, makwabta, da masu bukata. Manufar ita ce a tabbatar da cewa Musulmai marasa galihu suna farin ciki da samun naman da za su ci yayin bikin.
Dole ne dabbar da aka sadaukar da ita ta cika ƙa’idodi, waɗanda suka haɗa da cika shekarun da ake bukata kuma mafi inganci da ake da su.
6. Ana so maza da mata da yara su sanya tufafin da za su fita don halartar sallar idi. Shari’ah ta bukaci mata su fita su halarci sallar Idi. Wannan ya haɗa da mata masu aure, marasa aure, matasa, tsofaffi, da ma masu haila.
