Kasuwanci
IPMAN ta musanta zargin ƙara kuɗin Fetur zuwa Naira 700
Ƙungiyar dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN, ta musanta zargin da ake yi mata cewa za ta ƙara farashin man zuwa Naira 700 a kan kowacce Lita.
Shugaban ƙungiyar na shiyyar Kudu maso Yamma Mista Dele Tajuddeen, ne ya musanta batun ƙarin kuɗin a zantawar sa da manema labarai.
Haka kuma, ya buƙaci al’umma da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan karin kuɗin.
Ya ce, farashin Fetur ɗin ba zai wuce yadda ake sayar da shi ba a yanzu.
