Labarai
Kaduna: Ƴan bindiga sun gargaɗi mazauna Birnin Gwari
Mazauna yankin Birnin gwari da ke jihar Kaduna, sun koka da cewa, suna fuskantar barazanar rashin abinci sakamakon yadda ‘yan bindiga suka hana su zuwa gonakinsu.
BBC ta ruwaito cewa, mazauna yankin sun ce, ƴan bindigar sun sanya musu haraji tare da yi musu barazanar sace duk manomin da ya je gona da kuma cinye amfanin gonakinsu
Haka kuma ta ruwaito cewa, a tattaunawarta da Ɗan Masanin Birnin Gwari Zubairu Abdulra’uf Idris ya shaida mata cewa idan ba a ɗauki mataki ba kan wannan matsala za a samu yunwa a waɗannan wurare.
“Har yanzu manoma ba su kai ga gonakinsu ba domin a cikin kashi 100 na manoma kashi talatin ne suka samu suka je gonakinsu.
“Ga shi yanzu watan 7 ake ciki wanda idan nan da makoni biyu ko uku mutane ba su yi shuka ba, toh ina ganin sai dai kawai a hakura da noman”, a cewarsa.
