Labarai
Jam’iyyar APC Ta Nesanta Kanta Daga Nade-Naden Majalisun Kasa
Kwamitin gudanar ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar APC mai mulki ta nesanta kanta daga manyan mukaman shugabancin majalisar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas suka sanar.
Akpabio da Abbas sun sanar da samun sabbin shugabannin majalisar yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Akpabio ya ce sanarwar ta yi dai-dai da yarjejeniyoyin jam’iyyun masu rinjaye da na marasa rinjaye.
A majalisar dattawa, Akpabio ya bayyana Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti) a matsayin shugaban masu rinjaye; David Umahi (APC, Ebonyi), mataimakin shugaban masu rinjaye; Mohammed Ali Ndume (APC, Borno), a matsayin bulaliyar majalisa; da Lola Ashiru (APC, Kwara), mataimakin bulaliya.
Sanata Simon Davou Mwadkwon (PDP, Plateau North), shi ma an nada shi a matsayin shugaban marasa rinjaye.
Sauran shugabannin marasa rinjayen sun hada da Sanata Olalere Oyewumi (PDP, Osun West), mataimakin shugaban marasa rinjaye; Sanata Darlington Nwokocha (LP, Abia Central), bulaliyar marasa rinjaye da Sanata Rufai Hanga (NNPP, Kano ta tsakiya), mataimakin bulaliyar marasa rinjaye.
Tsagin marasa rinjaye a majalisar dattajai jam’iyyar PDP tana da sanatoci 36; LP, 8; SDP, 2; NNPP, 2; YPP, 1; da APGA, 1.
Kakakin majalisar Abbas ya nada Julius Ihonvbere (APC, Edo) a matsayin shugaban masu rinjaye; Abdullahi Ibrahim Halims, (APC, Kogi), mataimakin shugaban masu rinjaye; Usman Bello Kumo (APC, Gombe), bulaliyar majalisa; da Adewunmi Oriyomi Onanuga (APC, Ogun), mataimakin bulaliya.
Kingsley Chinda (PDP, Rivers), dan takarar tsohon gwamna, Nyesom Wike, ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar.
An nada Ali Madaki (NNPP, Kano) a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye; Ali Isa na PDP, bulaliyar marasa rinjaye; da George Ebizimawo na jam’iyyar Labour, mataimakin bulaliyar marasa rinjaye.
Shugaban majalisar ya ce dukkan ‘ya’yan jam’iyyar APC a majalisar sun amince da zaben shugabannin jam’iyya mai mulki.
Sai dai shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a jiya ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) ba ta da masaniyar bayyanar sunayen shugabannin majalisar wakilai ta kasa ta 10.
Da yake magana a wata ganawa da gwamnonin jam’iyyar da suka kasance ‘ya’yan jam’iyyar a sakatariyar APC ta kasa a ranar Talata a Abuja, Adamu ya ce jam’iyyar ba ta yi magana da shugabannin jam’iyyar a hukumance ba.
Ya ce, “A yanzu haka ina jin rade-radi daga kafafen yada labarai na yanar gizo cewa an yi wasu sanarwa a majalisar dattawa da ta wakilai.
“Shedikwatar jam’iyyar ta kasa, NWC, ba ta bayar da irin wannan bayani ba ko kuma ta sanar da zabar shugabannin. Kuma har sai mun yanke shawara da mu’amala da su a rubuce, wanda shi ne al’ada da aiki, ba nufin mu ba ne mu samu rabuwar kai. Don haka duk sanarwar da aka bayar ba daga wannan sakatariyar ba ce.”
