Labarai
Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Binciken Basussukan Da Masari Ya Ciwo
An baiwa Kwamitin damar binciken duk wasu basussukan da gwamnatin jihar Katsina, karkashin Dikko Radda ya gada.
An kuma baiwa kwamitin wata guda ya mika rahotonsa kamar yadda sakataren gwamnatin jihar, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin a Katsina, Arc. Dangiwa ya dora wa kwamitin alhakin tantance duk wani bashin da ake bin gwamnatin jihar, da tanadin kasafin kudin da aka yi na irin wadannan basussuka.
Ya ce adadin da aka biya zuwa yanzu, tare da nuna yanda za a yi idan irin wannan bashin ya fada karkashin tallafin hadin gwiwa ko kuma ya kasance karkashin tallafin Kungiyoyin duniya.
Sauran sharuddan kwamitin, a cewarsa, sun hada da sake duba tanadin kasafin kudi na irin wadannan basussukan da kuma shawarwari ga gwamnati, a inda ya dace, kan wasu hanyoyin samar da asusu domin daidaita kudaden da aka tabbatar.
Kwamitin ya hada da Arch. Almajir Salihu a matsayin shugaba, tare da injiniya Sani Magaji, Shamsuddeen Sanusi Ahmad, Suleiman Musawa, injiniya Babangida Yahaya Abubakar and Arch. Bashir Muhammad Idris, da sauran su, mataimakin gwamnan jihar.
Mallam Faruk Lawal Jobe, ya ce kwamitin ya dogara ne akan kudirin gwamnati na tabbatar da adalci da kuma sauraren shari’un ‘yan kwangilar da ke da hakki.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa mambobin kwamitin za su kasance daidai da aikin bisa la’akari da kwarewa da jajircewa na su.
Mataimakin Gwamnan ya bukace su da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu tare da gabatar da rahotonsu cikin lokacin da aka kayyade.
