Uncategorized
Nasarawa: Likitoci Sun Dakatar Da Yajin Aikin Gargadi Da Suka Fara
Kungiyar likitoci ta Kasa reshen jihar Nasarawa, ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar, inda ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu da ta biya musu dukkan bukatunsu.
Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne biyo bayan gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da karin girma ga wasu mambobin kungiyar har na tsawon shekaru tara da karin shekara sama da shekaru 12.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron gaggawa na majalisar gudanar a garin Lafia babban birnin jihar a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar jihar, Dakta Peter Attah, ya bayyana cewa sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar domin rage radadin al’ummar jihar.
Attah ya ce kungiyar ta umarci mambobinta da su koma bakin aiki cikin gaggawa a jihar domin ceton rayuka.
Ya ce, “A karshen mako biyu, idan har gwamnatin jihar ba ta biya mana bukatunmu ba, za a iya barin mu da wani zabin da ya wuce mu shiga yajin aikin da ba a taba gani ba har sai an biya mana dukkan bukatunmu.
Daily Trust ta tuna cewa tun a ranar 13 ga watan Yunin 2023 kungiyar ta ba da wa’adin kwanaki 21 na ta mika bukatar ta kafin yajin aikin gargadi.
