Labarai
NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya 146 Da Aka Dawo Da Su Daga Jamhuriyar Nijar
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) ta karbi wasu ‘yan Najeriya da suka makale a Yamai na Jamhuriyar Nijar.
Dokta Nuraddeen Abdullahi, ko’odinetan hukumar NEMA a ofishin reshen jihar Kano ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar mutanen da suka dawo a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano.
Mutanen da suka dawo sun isa ne a cikin jirgin SKY MALI na kamfanin Ethiopian Airline B737-400 mai lamba UR-CQX da misalin karfe 10:35 na safe.
Wadanda aka dawo da su sun hada da manya maza 56, manya mata 39 da yara 51 (mace 35 da maza 16) daga sassa daban-daban na Najeriya musamman Katsina, Kano, Adamawa, Legas, Imo, Enugu da jihar Edo da dai sauransu.
Abdullahi ya ce an dawo da ‘yan gudun hijirar ne ta hanyar wani shiri na mayar da ‘yan gudun hijira bisa radin kansu karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya (IOM).
Ya kara da cewa shirin an yi shi ne ga ‘yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali da suka bar kasar don neman wuraren kiwo a kasashen Turai daban-daban amma ba su da karfin dawowa lokacin da tafiyar tasu ta samu tangarda.
Abdullahi ya kuma shawarci matasan Najeriya da su guji jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar tafiye-tafiyen neman wuraren neman kudi a wasu kasashe.
Mista Emeka Njoku daga jihar Imo da ya ke ba da labarin irin halin da su ke ciki, ya ce ya je kasar Tunusiya ne watanni hudu da suka wuce domin neman wuraren sana’a.
NJoku ya yi kira ga gwamnati da ta samar da guraben ayyukan yi da karfafawa ‘yan Najeriya.
