Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa Ta Gudanar Da Ganawar Sirri Kan Sunayen Ministoci

Majalisar dattawan a tsakar ranar yau ta shiga wani zaman sirri na ‘yan mintoci kafin fara zaman majalisar na yau, wanda jerin sunayen ministocin da ake kyautata zaton fadar shugaban kasa ya isa hannun Majalisar.

Jim kadan bayan karbar koke, wanda shine abu na biyar a cikin takardar, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ya kamata Sanatocin su shiga wani ganawa bayan shugaban, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya) ya bayyana hakan.

Majalisar dattijan ta shiga zaman sirrin da karfe 11.59 na rana.

Majiyar mu ta gano cewa taron na iya kasancewa akan wadanda aka nada a matsayin ministoci daga shugaba Bola Tinubu.

Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa tuni jerin sunayen suka fara haifar da matsala a tsakanin Sanatocin, wanda ya bayyana bukatar yin taron.

Ku tuna cewa akwai wata ganawa da shugaban majalisar dattawa ya yi da manyan masu ruwa da tsaki a jiya. Ya dauki tsawon sa’o’i da yawa ana yin sa.

Majiyar ta shaida cewa Shugaban Majalisar ya riga ya mallaki jerin sunayen, wanda za a iya karantawa bayan ganawar sirri, ko kuma a mako mai zuwa tunda ba za a yi zaman majalisar ba a gobe.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet