Labarai
Wani Jigon APC Ya Bukaci A Rusa Shugabancin Jamiyyar
Wani jigo a jamiyyar APC a jihar Zamfara Ahmad Dan Wudi ya Mika takardar Kokensa ga sakatariyar Jamiyyar ta kasa, inda ya bukaci rushe dukkanin shugabancin Jamiyyar daga Kasa har sama a jihar.
Takardar koken Daya aika ta ga mukaddashin Shugaban Jamiyyar, wadda majiyar mu ta sama, tana dauke da bayanan yadda aka gudanar da zaben 2023, da yadda Jamiyyar Tasha Kaye.
“A matsayina na dan jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ina mika koke ga ofishinku a rubuce cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Zamfara amma ta sha kaye a zaben gwamna saboda sakaci da shugabannin jam’iyyar na jihar suka yi.
“Hakazalika, yana da mahimmanci a sanar da ku cewa jam’iyyar tun daga matakin Unguwa da Kananan Hukumomi da Jihohi ba sa gudanar da taron shugabanni ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada, wanda hakan ya sa jam’iyyar ta tsinci kanta a cikin halin kaka-ni-kayi a jihar.
“Na kuma lura da takaicin cewa tun lokacin da shugaban jam’iyyar na jihar, Tukur Umar Danfulani ya hau kan karagar mulki, bai zauna a ofishin ba wanda ke nuna rashin jajircewa,” inji shi.
Ya ce bisa ga abin da ake zargin ‘ya’yan jam’iyyar APC na Zamfara na kira gare ku da ku yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ba ku, ku rusa shugabannin jam’iyyar tun daga matakin unguwanni da kananan hukumomi da jiha domin jam’iyyar ta samu hadin kai da kuma gaggarumi.
