Featured
Davido Na Cigaba Da Shan Suka Kan Bidiyon Wakar ‘Cin Zarafin Musulunci’
Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, na ci gaba da shan suka daga Musulmai a shafukan sada zumunta, bayan sakin wani bidiyon waƙa na tsawon mintuna 45 a Twitter.
Musulmi da dama sun bayyana bidiyon wakar a matsayin abin takaici da kuma cin fuska ga Addinin Musulunci.
A farkon wakar waƙar da ya saki, an nuna wasu sanye da shiga irin ta Musulmai suna sallah kuma suna tiƙar rawa, lamarin da Musulmi ke ganin mawakin ya zarce makaɗi da rawa.
Sun zargi Davido, wanda ke da mabiya kusan miliyan 14 a intanet, da rashin mutunta addinin Musulunci ta hanyar haɗa ibadarsu da al’adarsu tare da waƙa da raye-raye. Sun kuma ja hankalin mawakin da ya goge bidiyon wakar tare da bai wa ɗaukacin Musulmi hakuri.
Bayan Musulumi sun bayyana fushinsu da kuma irin suka da mawakin ya sha kan bidiyon ne ya goge wakar daga shafin nasa.
Al’amarin dai na ci gaba da haifar da zazzafar muhawara da musayar ra’ayi a tsakanin mabiya Davido da wasu fitattun masu fada a ji Musulmi a kafafen sada zumunta.
Daga cikin su akwai Bashir Ahmad da fitaccen jarumin Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu.
