Featured
Hisbah Ta Kama Wasu Mutane Da Ake Zarginsu Da Yunkurin Auren Jinsi
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin shirya auren jinsi.
Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar.
Ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa an ga wasu samari biyu masu suna Khalifa da Abubakar suna kokarin sumbatar juna a yayin wani biki, wanda ake zargin bikin aurensu ne.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta zargin cewa taron bikin ranar haihuwa ne ba bikin aure ba kamar yadda suka yi ikirari.
A cewar daya daga cikin wadanda ake zargin, khalifa, shi ne ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa, sai abokinsa Abubakar ya ba shi kek a bakinsa wanda ya yi amfani da bakinsa wajen bashi.
Daurawa ya ce mutanen biyu suna hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.
