Labarai
An kai ruwa rana tsakanin DSS da jami’an gidan yari kan wanda zai tafi da Emefiele
An kaure da kokawa a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas a ranar Talatar nan lokacin da jami’an tsaron farin kaya (DSS) da jami’an hukumar da ke kula da gidan gyaran hali da tarbiyya ta Kasa (NCC) suka yi artabu kan tsare Godwin Emefiele.
Emefiele wanda dakataccen gwamnn babban bankin Kasa CBN ne, a yau an gurfanar da shi a Kotu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Emefiele wanda ke tsare a hannun DSS tun a watan Yuni ya gurfana a gaban kotu ranar Talatar nan.
Mai shari’a Nicholas Oweibo ya bayar da belin tsohon gwamnan CBN din da aka dakatar a kan Naira miliyan 20.
Sharadin belin dai ya hada da bayar da wanda zai tsaya masa kuma kaddarorinsa za su zama a karkashin ikon kotun da ke Ikoyi a Legas.
Haka kuma zai ajiye fasfo dinsa da kuma samar da ma’aikacin da bai gaza mataki na 16 ba don samun cikakken belin.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Emefiele a gidan yari har sai an cika sharuddan belinsa.
Sai dai maimakon a bada gwamnan babban bankin ga jami’an gidan yari, hukumar DSS ta yi yunkurin dauke shi, lamarin da ya ci tura.
A yayin da ake samun sabani ne, rigar wani jami’in gidan yarin ya yage, wanda ya nuna singiletin da ke cikin kayansa.
Jami’an DSS da ke da makamai sun zarce yawan jami’an gidan yarin.
