Featured
Kotu ta bayar da belin Emefiele kan Naira Miliyan 20
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas a ranar Talatar nan ta bayar da belin gwamnan babban bankin Kasa CBN Godwin Emefiele da aka dakatar.
Kotun ta bada belin Emefiele a kan kudi Naira miliyan 20 tare da mutum guda daya da zai tsaya masa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bayar da belinsa ne bayan ya ki amsa laifuffuka biyun da ake tuhumarsa da su wadanda ke da alaka da mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.
Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da mallakar bindigogi da alburusai ba bisa ka’ida ba wanda ma’aikatar shari’a ta tarayya ta fi son a yi masa a gaban alkali mai shari’a Nicholas Oweibo.
