Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Bude Cibiyoyin Horas Da Sana’o’in Da Ganduje Ya Rufe

 

Gwamnatin jihar Kano a ranar Alhamis din nan ta sanar da bude cibiyoyin koyan sana’o’in dogaro da kai guda 26 da gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ta rufe.

Kwamishinan ayyuka da gidaje, Alhaji Marwan Ahmad ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Kano.

Ya ce gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce ta kafa cibiyoyin tare da baiwa matasa da mata damar koyan sana’o’i daban-daban.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a bude dukkanin cibiyoyin kasuwancin guda 26 da gwamnatin Sanata Kwankwaso ta kafa wadanda gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da su.

“Cibiyoyin sun hada da: koyar da aikin Jarida, Noma, kiwon Kaji, Tuki, Gyaran hali, kula da baki da yawon bude ido, Kiwon Dabbobi, Wasanni, Ilimi, Tsaro na kamfanoni, da sauransu,” in ji shi.

A cewarsa, za a yi amfani da cibiyoyin da kyau wajen magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da ‘yan daba da ke damun mazauna jihar.

Ya ce gwamnan ya kuma umarci ’yan kwangilar da ke tafiyar da ayyukan titin kilomita 5 da gwamnatin Kwankwaso ta fara a fadin kananan hukumomin jihar 44, da su koma bakin aiki a wuraren.

Ahmad ya ci gaba da cewa, haka ma gwamnatin jihar ta koma bakin aiki a aikin kogin Jakara da aka yi watsi da shi a cikin birnin Kano.

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’umma.

“Samar da kayayyakin more rayuwa zai zaburar da ayyukan zamantakewa da tattalin arziki na jihar da kuma tushen kudaden shiga da kuma ci gaban al’umma baki daya”. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet