Labarai
Yan Najeriya Za Su Ga Amfanin Cire Tallafin Mai Nan Gaba — Gwamnan Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya ce nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su gane alfanun cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron karrama shi da al’ummar Hadejia suka shirya a karshen mako.
A cewarsa: “Dole ne mu yi haƙuri. Ina mai tabbatar muku da cewa nan ba da jimawa ba sauye-sauye masu raɗaɗi da gwamnatin APC ta yi za su haifar da kyakkyawan sakamako.
“Shugaba Tinubu yana da kyakkyawar manufa ga Najeriya; don haka yana bukatar cikakken goyon bayan ’yan Najeriya don aiwatar da manufofinsa na inganta Najeriya.
“Abin da ake bukata daga ‘yan Najeriya shi ne fahimta da goyon baya. Ba da daɗewa ba, za ku zama ainihin masu cin gajiyar cire tallafin.”
Tun da farko, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa masu jituwa ta kasa, Dakta Bature AbdulAziz, ya bukaci gwamnan da ya fito da wani shiri da zai rage yawaitar hijirar da matasa ke yi daga jihar zuwa kudancin kasar nan.
