Labarai
Yan Sanda Sun Cafke Mutum Biyar Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mai Awara
Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da cin zarafin wata karamar yarinya ta hanyar yi mata fyade.
Kakain rundunar yan sanda DSP Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da kama mutane a wata sanarwar da ya aikewa manema labarai a ranar Talatar nan.
Sanarwar ta ce wani mutum mai suna Idris Muhammad Munkaila mai shekaru 50 da ke Yola a karanar hukumar Jahun, ya kai rahoto ofishin yan sanda da ke Jahun cewa a ranar 28 da watan Yuli da misali karfe 20:30 ‘yarsa wadda aka boye sunanta ta fito domin suyar Awara.
Tana cikin suyaf ne wani mai suna Aliyu Sani mai shekaru 50 ya kaita dakin Rabi’u Ibrahim mai shekaru 45 duk a karamar hukumar Jahun kuma duk dinsu sun santa.
A binciken da sashin binciken manyan laifuka na shedkwatar rundunar yan sandan jihar Jigawa ya gudanar ya nuna cewa, wani Idris Haruna mai shekaru 38 da Rabi’u Inuwa mai shekaru 50 da kuma Hussaini Mato mai shekaru 32 duk a garin Jahun da ke karamar hukumar Jahun sun yi lalata da ita a wannan kwanan wata, lokaci da kuma wuri.
Haka kuma, an kai dukkan wadanda ake zargin da wadda aka aikatawa abun cibiyar bada agajin gaggawa na jihar da ke Dutse (SARC Dutse) domin duba lafiyarsu.
A yayin da ake duba lafiyar daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Aliyu Sani mai shekaru 50 da haihuwa, yana dauke da cutar Kanjamu, yayin da wani Rabi’u Inuwa mai shekaru 50 yana dauke da cutar ciwon Hanta.
DSP Lawan ya bayyana cewa wani abun farin ciki wadda aka aikatawa laifin an gwadata bata dauke da kowace cuta.
Ya kuma tabbatar a cikin sanarwar ceqa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya domin girbar abun da suka shuka.
