Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Siyo Hatsi Don Siyarwa Al’umma A Rahusa

Da ta kuduri aniyar samar da matakan rage radadin cire tallafin man fetur, gwamnatin jihar Kano ta shirya sayan hatsi daga gwamnatin tarayya tare da sayar wa manoma a kananan hukumomi 44 a kan farashi mai sauki.

Gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa na farko da mambobin kwamitin sake farfado da hanyar tallafawa al’umma na gwamnati daga kananan hukumomin 44 da ya gudana a gidan gwamnati na Africa House.

Abba Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta damu da irin matsalolin da mutane ke fuskanta sakamakon tsadar sufuri da kayan abinci, saboda cire tallafin, inda ya yi alkawarin lalubo wasu hanyoyin da za a magance matsalar.

Gwamnan ya kara da cewa, ana shirin dawo da motocin Kanawa domin taimakawa dalibai, mata, da sauran bangarorin jama’a da ke bukatar sufuri mai sauki.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Dangane da zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Kasa NLC da za ta yi a fadin kasar a ranar Larabar nan, gwamnan ya yi kira da kakkausar murya ga shugabannin kwadagon da su yi hakuri tare da dakatar da yajin aikin da suka shirya gudanarwa a daidai lokacin da gwamnati a dukkan matakai ke dukufa wajen samar da hanyoyin da za a rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta sakamakon tashin farashin man fetur.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet