Connect with us

Labarai

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Sanya Tukuici Ga Wanda Ya Bata Bayanan Wasu ‘Yan Daba

 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ana neman wasu manyan ‘yan daba guda uku tare da yi wa duk wanda ya kawo bayanan inda za’a same su alkawarin bashi kyautar Naira 100,000 a cikin kwanaki bakwai daga ranar Larabar nan 3 ga watan Agusta 2023.

Kwamishinan yan sanda CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a bikin bude wasan sada zumunta tsakanin rundunar ‘yan sanda da tubabbun yan daba a Kano ranar Laraba.

Gumel ya bayyana cewa ana neman ‘yan dabar ne bayan sun ki ba su hadin kai su fito domin tattaunawa da ‘yan sanda duk da cewa ‘yan daba 99 ne suka bayyana a lokacin da rundunar ‘yan sandan ta gayyaci mutum 30 kacal.

Ya yi bayanin cewa ’yan daba uku da suka hada da Barakata na Dorayi Quarters, Hantar Daba da Chile Mai Doki na Tudun Fulani, sun nuna taurin kai ne kuma suka ki saukar da makamansu ga ‘yan sanda domin su tuba.

“Wannan wasan kwallon kafa da rundunar ‘yan sanda da kungiyar YOSPIS suka shirya an yi shi ne da nufin samar da zaman lafiya da kuma maraba da dawowar matasan da suka shiga harkar daba.

“Mun yi kokarin ganin Kano ta kubuta daga aikata laifuka ta hanyar tattaunawa da kuma hanyoyin lumana domin karfafa wa matasa gwiwa wajen gujewa munanan abubuwa da suka hada da shaye-shayen miyagun kwayoyi, satar waya, ‘yan fashi da sauran laifuka da aka gano tare da su.

“Mun gayyato su 30 din zuwa ga umurnin da muka bayar amma ga mamakinmu 99 daga cikinsu sun zo sun kaurace wa munanan ayyuka tare da mika makamansu.

“Akwai mashahuran mutane uku da muka yi duk kokarin gayyatarsu amma sun ki zuwa, a cikin mutanen Barakata na Dorayi Quarters, Hantar Daba da Chile Mai Doki na Tudun Fulani, An ayyana su amatsayin wadanda ake nema ruwa ajallo.

“Dangane da aikin ‘yan sandan al’umma, duk wanda ya kawo daya daga cikinsu za a ba shi Naira 100,000. Wannan kudi za su fito daga aljihuna.

“Idan al’ummomin sun kawo wadannan ‘yan baranda da ake nema a cikin aikin dan sandan al’umma, za su karbi N300,000 a wurina,” in ji CP.

Da take gabatar da nata jawabin babbar daraktar kungiyar matasa mai yaki da cututtuka masu yaduwa da al’umma (YOSPIS), Zainab Ahmad ta bayyana cewa wasan kwallon kafa na da burin ganin an samar da zaman lafiya a jihar ta hanyar rungumar matasa masu aikata miyagun laifuka tare da nuna musu cewa har yanzu ana musu barka da dawowa cikin al’ummarsu.

Tun da farko a sakon sa na fatan alheri babban daraktan ayyuka na musamman na Kano, AVM Ibrahim Umar wanda ya wakilci gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin dadinsa da kokarin da ‘yan sanda suka yi na kwato matasa daga wannan hali na rashin gaskiya, yayin da ya kuma yabawa kungiyar ta YOSPIS bisa shirya wannan wasa na sada zumunci.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da tarin kayayyaki ga matasa domin yaba kokarin ‘yan sanda a jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet