Featured
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga Ministocinsa
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aikewa majalisar dattawa sunan tsohon Ministan ƙwadago na kasa Festus Keyamo domin amincewa da shi don nada shi a matsayin minista.
Haka Kuma Shugaba Tinubu ya aike da sunan Dr. Mairiga Mahmud domin maye gurbin Maryam Shetty daga Kano wadda aka tura sunanta a ranar Larabar data gabata.
Tinubu ya aike da sunayen ne ta cikin wata wasika da ya aikewa majalisar dattawa kuma Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya Karanta a zaman majalisar na yau juma’a.
