Labarai
Karon Farko Ganduje Zai Jagoranci Taron NWC A Matsayin Shugaban APC
Sabon shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, a ranar Talatar mai zuwa zai gana da mambobin kwamitin ayyuka na kasa NWC a wani aiki na farko da zai fara a matsayin shugaban riko na jam’iyyar.
Lamarin ya zo ne kwanaki biyu bayan amincewa da tsohon gwamnan jihar Kano a wajen taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa karo na 12 da ya gudana a Transcorp Hilton da ke Abuja.
Baya ga Ganduje, Kakakin Majalisar Dattawa ta 9, Sanata Ajibola Basiru, shi ma an amince da shi a matsayin sabon sakataren jam’iyyar APC na kasa a yayin taron NEC na ranar Alhamis.
A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilinmu, wani jigo a jam’iyyar ta APC da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa dan siyasar na jihar Kano mai shekaru 73, zai jagoranci taronsa na farko a shedikwatar jam’iyyar ta kasa ranar Talata.
Ya ce, “Za mu yi taron NWC ranar Talata. Zai kasance taron Ganduje na farko a hukumance.
“Na tabbata wani kokari ne a bangarensa na sanin ‘yan kwamitin a cikin kwanciyar hankali biyo bayan damuwa da taron majalisar NEC ya amince da nadin nasa.
“Basiru ya kuma yi alkawarin kasancewa a wurin taron.
Jaridar Punch ta rawaito cewa A kan abin da zai kasance ajandar taron, jigon jam’iyyar ya bayyana cewa za a ba da fifiko wajen nada jami’an da mukamansu ba kowa a cikin na NWC.
