Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Mace Ta Farko A Matsayin Babbar Alkaliyar Jihar

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da mai shari’a Dije Audu Aboki a matsayin mace ta farko da ta zama shugabar alkalai a jihar.

Bikin ya gudana ne a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin din nan, inda gwamna Yusuf ya bukaci bangaren shari’a da su marawa kokarin gwamnatin sa na ruguza gine-gine da kuma kwato kadarorin al’umma da ake zargin gwamnatin da ta shude ta samu ta hanyar da ta saba doka.

Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati uku.

“Dangantakar da ke tsakanin bangaren shari’a, majalisa, da zartarwa ba gasa ba ce, amma mai darewa ce,” in ji shi.

Ya bayyana kudurinsa na ci gaba da kyautata alaka a tsakanin wadannan rassa.

Gwamnan ya yaba da sadaukarwar da Mai Shari’a Aboki ta yi a fannin shari’a, inda ya ce, “Mai shari’a Aboki ta biya yi aiki tukuru a shari’a ta hanyar nuna kwarewa, hazaka, da kishin kasa cikin ikon Allah ya daukakata a matsayin babban alkaliyar jihar”.

A yayin da yake tinkarar kalubalen samar da adalci cikin gaggawa, Gwamna Yusuf ya bayyana bukatar a gaggauta magance miyagun laifuka, inda ya ce, “Ra’ayinmu ne idan aka gaggauta aiwatar da irin wadannan shari’o’in kuma aka hukunta wadanda aka samu da laifi, hakan zai hana wasu da ke fatan shiga cikin lamarin aikata laifuka”.

A nata martanin, babban alkaliyar kotun mai shari’a Aboki, ta nuna jin dadinta da samun damar yin aiki tare da yin alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a cikin aikinta.

Ta bayyana aniyar ta na dawo da martabar shari’a da aka rasa a jihar Kano tare da yin kira da a ba su goyon baya da hadin kai daga bangaren zartarwa, ‘yan majalisu da na shari’a, da kuma hukumomin kwararru.

Sabuwar Babbar Alkalin ta yi alkawarin dawo da martabar bangaren shari’a.

A yayin kaddamar da Mai Shari’a Aboki, jihar Kano ta dauki wani muhimmin mataki na inganta bambancin jinsi da karfafa tsarin doka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet