Labarai
Kotun Shari’ar Musulunci Ta Tsare Wani Lebura Kan Zargin Satar Ganda
An gurfanar da wani matashi dan shekara 23 mai suna Abdulwahab Yusuf a gaban wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kano a ranar Talatar nan.
An gurfanar da matashin ne bisa zargin satar fatar saniya, (Ganda) wadda kudinta ya kai Naira 8,500.
Yusuf wanda ke zaune a unguwar Tukuntawa Quarters da ke jihar, an tuhumi shi ne da laifin sata.
Alkalin kotun, Umar Lawal-Abubakar, ya bayar da umarnin a tasa keyar wanda ake kara, wanda ya amsa laifinsa zuwa gidan yari.
Lawal Abubakar ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 22 ga watan Agustan da muke ciki domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Tun da farko, mai gabatar da kara Insifekta Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara, Fatihu Auwal, kuma yana zaune ne a Tukuntawa Quarters, ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Fagge, a jihar Kano, a ranar 5 ga watan Agusta.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Wada ya ruwaito cewa wanda ake tuhumar ya shiga turakar mai karar ya sace fatar fatar saniya da aka babbake wato Ganda. (NAN)
