Featured
ECOWAS Ta Samu Rabuwar Kai Kan Matakan Da Ya Kamata A Dauka Akan Nijar
Majalisar koli ta kungiyar tattalin arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta samu rabuwar kawuna kan matakan da ya kamata a dauka domin tunkarar juyin mulkin Nijar.
Yayin da wasu ‘yan majalisar ta ECOWAS ke goyon bayan matakin soji a kan gwamnatin Nijar, wasu kuma na adawa da hakan.
‘Yan majalisar dokokin kasar 22 ne suka halarci taron na musamman a yau Asabar din nan domin tattauna rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar.
Yayin da wasu daga cikin ‘yan majalisar suka yi jawabin goyon bayan tattaunawar diflomasiyya, wasu kuma sun yi kira da a dauki matakan da za su dakile yunkurin gwamnatin soja a yankin.
