Connect with us

Labarai

Yanzu-Yanzu: Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari, NAF Ta Tabbatar

Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da cewa daya daga cikin jirginta ya yi hatsari a jihar Neja ranar Litinin din nan.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Rundunar sojin saman ta ce jirgin na cikin aikin kwashe mutane ne a lokacin da hadarin ya afku.

Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Litinin din nan, ta ce jirgin ya taso ne daga makarantar firamare ta Zungeru a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna amma daga baya aka rawaito cewa ya yi hatsari a wani kauye da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

A wani bangaren sanarwar ta bayyana cewa, “Jirgin saman mai saukar ungulu kirar MI-171 na rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a yau, 14 ga watan Agusta, 2023, da misalin karfe 1:1.00 na rana a kauyen Chukuba a jihar Neja.

“Jirgin ya taso ne a makarantar firamare ta Zungeru a kan hanyar Kaduna, amma daga baya aka gano cewa ya fado kusa da kauyen Chukuba a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.”

Gabkwet ya ce ana ci gaba da kokarin ceto matukan jirgin da fasinjojin da ke cikin jirgin.

Sanarwar ta kara da cewa, “A halin yanzu ana ci gaba da kokarin ceto ma’aikatan jirgin da fasinjojin da ke cikin jirgin mai saukar ungulu, yayin da aka fara gudanar da bincike na farko don gano musabbabin hadarin.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet