Featured
Tawagar ECOWAS Ta Koma Nijar Don Ganin An Shawo Kan Rikicin Dake Faruwa A Ƙasar
Tawagar shiga tsakani na Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta isa Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin ganin an shawo kan dambarwar siyasar ƙasar ta hanyar lumana.
Tun bayan saukarta a filin jirgin saman Yammai, tawagar ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.
Ana sa ran za su tattauna da jagoran mulkin soja, Janar Abdourahmane Tchiani, game da yadda za a mayar da mulki ga farar hula.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalami Abubakar na kuma dauke da mai alfarma Sarkin Musulmin kasar, Muhammad Sa’ad Abubakar tare da wasu jami’an ECOWAS.
