Connect with us

Featured

Ƙungiyar mawallafa jaridun yanar gizo ta miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar wakilin Jaridar Leadership

Shugabancin riƙo na ƙungiyar mawallafa jaridun yanar gizo wato Chartered Online Publishers ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Abdullahi Yakubu, wakilin Jaridar Leadership a Kano, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a 18 ga watan Agusta, 2023.

Hakan na ƙunshe cikin wata Sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na riƙo Abdullateef Abubakar Jos, ya raba wa manema labarai

Jos ya ce rasuwar Abdullahi Yakubu babbar asara ce ga aikin jarida a Kano da ma Najeriya baki daya duba da irin gudunmawar da ya bayar yayin gudanar da aikinsa.

Ƙungiyar ta kuma jajantawa ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya da ta ƴan jaridu reshen jihar Kano wato correspondent chapel.

Sanarwar ta ƙara da cewa mambobin ƙungiyar Chartered Online Publishers ta Kano da shugabanninta sun kaɗu matuƙa da samun labarin rasuwar babban abokin aikin nasu, tare da bayyana cewa Abdullahi Yakubu yana da jajircewa a bangarensa na aikin jarida tun zamanin da ya yi aiki a kamfanin buga jaridu na Triumph .

A ƙarshe ƙungiyar ta yi addu’ar Allah ya baiwa iyalan mamacin haƙurin jure wannan babban rashi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet