Labarai
Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan N700m Na Daliban Jami’ar BUK ‘Yan Jihar
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da fitar da Naira miliyan 700 domin biyan kudin makaranta ga ‘yan asalin jihar 7,000 da ke karatu a Jami’ar Bayero Kano (BUK).
Gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a daren ranar Litinin, a shafin sa na Facebook da aka tabbatar.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano ta bakin kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Kofar Mata, ta shiga tattaunawa da jami’ar Bayero Kano kan matakan da za a dauka na rage sama da kashi 100 na kudaden makaranta wanda ake ganin zai iya sa dalibai da dama su daina karatu.
Hakazalika, hukumar jami’ar a matsayin wani mataki na magance karin kudaden da ta ce ya zama dole idan aka yi la’akari da kudaden da ta kashe ta kafa tsarin bayar da tallafin karatu ta hanyar bayar da kudaden gudanar da jami’ar da ta samu daga masu hannu da shuni.
A cikin sakon da Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce amincewa da Naira miliyan 700 na biyan kudin makarantar daliban Kano a jami’ar BUK.
An amince da shi ne a taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata duba da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da hanyoyin biyan kudin.
