Labarai
Hukumar EFCC Ta Cafke Wasu Mutane 23 Bisa Zargin Damfarar Intanet
Jami’an Hukumar EFCC na Jihar Sakoto, sun kai samame tare da cafke wasu mutane 23 da ake zargi da damfara ta yanar gizo
Bayan binciken kwakwaf da jami’an leken asiri suka yi tare da sanya ido ya tabbatar da cewa matasan na rayuwa fiye da yadda suke ba tare da wata hanyar samun kudin shiga na gaske ba
Hakan ya sa jami’an hukumar suka kutsa kai tare da cafke masu laifin yayin da ake ci gaba da bincike
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa EFCC na Jihar Sakoto, sun kai samame tare da cafke wasu mutane 23 da ake zargi da damfara ta internet da aka fi sani da ‘Yahoo boys’ a unguwar Bafarawa da ke cikin birnin Sakkwato.
Wata majiya daga ofishin shiyyar hukumar ta EFCC da ke Sokoto ta ce baya ga yankin Bafarawa, an kuma kai samame a yankin kalkalawa jihar Sokoto bayan binciken da jami’an leken asiri suka yi tare da sanya ido sosai ya tabbatar da cewa matasan na rayuwa fiye da yadda suke ba tare da wata hanyar samun kudin shiga na gaske ba.
Hakan a cewar majiyar, ya sa jami’an hukumar suka kutsa kai tare da cafke su yayin da ake ci gaba da bincike.
Wadanda aka kama sun hada da; Joy Ofem, Azeez O. Naimot, Ibrahim Amadu, Aigbekan Daniel, Adedayo Michael, Imran Mubaraq da kuma Oliyide Habeeblah.
Sauran sun hada da Wasiu Lukman Adekunle, Musa Abdulaziz, Abdullahi Ibrahim, Adejoh Nebiu Muhammad, Ibrahim Mubarak, Ahmed Ibrahim Abdullahi, Abdullahi senusi Adejoh da Umar Idris.
Cikin jerin sunayen akwai Muhammad Nuhu da Faisal Ahmed da Aliyu Ismail da Elijah Adebayo da Abubakar Bashir da Sakariya Ibrahim da Balogun Abdulayyan da kuma Buni Husaini.
Wasu daga cikin abubuwan da aka kwato sun hada da; wata motar Red Corolla sport 2009 model, White Corolla 2015 model, kwamfutar tafida gidanka 16 iri daban-daban,injin janareta 1 , wayoyin salula kala daban-daban guda 30 da kuma MTN Routers guda 2.
Sai dai majiyar ta bayyana cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala cikakken bincike.
