Labarai
Kwastam Ta Kama Fakitin Tabar Wiwi Da Wasu Kwayoyi 371 A Kebbi
A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi, hukumar kwastam ta Kasa, reshen jihar Kebbi, ta sake kwace fakiti 371 na tabar wiwi da kuma fakiti 98 na diazepam.
Kamen wanda aka yi a cikin kwanaki 10 da suka gabata wanda hukumar ta yi.
Kayan da aka kama sun hada da buhu 10 na wasu haramtattun kayayyaki, da fatar jaki guda 1080, buhunan shinkafar kasar waje 37, da buhun kayan sawa guda 16, da lita 300 na Motocin Man Fetur da kuma mota kirar Toyota Corolla.
Kwamandan hukumar kwastam na jihar Kebbi, Dakta Ben Oramalugo a lokacin da yake mika magungunan ga kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Usman Suleiman, ya ce adadin magungunan da aka kama ya kai miliyan casa’in da hudu da Naira dubu dari takwas da hamsin da hudu, da dari hudu da tara kacal.
A cewarsa, “Ku tuna cewa kwanaki goma da suka gabata, daidai ranar 14 ga watan Agusta, 2023, a yayin ganawa da manema labarai na karshe, mun sha alwashin cewa, daga yanzu ba za a samu sararin numfashi ga masu fasa-kwauri a rundunar ta Kebbi ba, musamman masu safarar kwayoyi da sauran kayayyaki masu cutar da lafiyarmu da tattalin arzikin kasa.
“Don haka, mun umurci jami’an mu da su kara sanya ido a duk lunguna da sako na jihar, bayan sun samu sahihin bayanai.
“Kudirin harajin kayayyakin da aka kama ya kai naira miliyan dari da sittin da hudu, dubu dari takwas da sha biyar, da dari shida da ashirin da tara.”
Tun da farko a nasa jawabin, CAC ta jajantawa iyalan ma’aikatansa biyu da suka rasa rayukansu a hanyar Bunza, Koko, Dakingari a ranar Alhamis.
