Labarai
Gwamnan Bauchi Ya Bada Umarnin Rufe Wata Makaranta Nan Ta Ke
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya bayar da umarnin rufe wata makaranta nan ta ke bisa mutuwar wani dalibi
Daukar matakin ya biyo bayan ta’asar da wasu da ake zargin matsafa ne suka aikata wa dalibin
Gwamnati ta umarci jami’an tsaro a jihar da su kara kaimi wajen cafko wadanda suka aikata wannan ta’asa
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya bayar da umarnin rufe wata makaranta cikin gaggawa da wani matashi mai suna Mohammed Abidin Musa ya mutu.
An tsinci gawar Musa a cikin makarantar, tare da cire wasu muhimman sassan jikinsa da wasu da ake zargin matsafa ne suka aikata.
Sai dai har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai game da lamarin har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Gwamnan ya bada umarnin ne a ranar Laraba a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan mamacin a Gidan Bare-Bari.
Ya samu rakiyar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Awal Musa Mohamed da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS.
A yayin da yake jajanta wa ‘yan uwa mamacin, Mohammed ya yi kira ga iyaye da su sanya ido a kan motsin unguwanninsu.
Ya umarci jami’an tsaro a jihar da su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Ya ce makarantar za ta ci gaba da kasancewa a rufe domin zurfafa bincike, inda ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da jami’an tsaro domin ganin an gurfanar da masu laifin.
