Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa Za Ta Binciki Wasu Ayyuka 10,000 Da Aka Yi Watsi Da Su

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Dr. ‘Lere Oyewumi, ya bayyana shirin da majalisar kasa ta 10 ta ke yi na gudanar da bincike kan ayyukan gwamnatin tarayya da aka yi watsi da su a fadin kasar nan.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Oyewumi, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Osun ta Yamma, ya bayyana hakan a Ikire ranar Juma’ar nan lokacin da yake zantawa da manema labarai.

A cewarsa, akwai ayyuka sama da 10,000 da Gwamnatin Tarayya ke daukar nauyinsu da aka yi watsi da su a duk sassan kasar nan.

Ya kuma ce ‘yan majalisar za su yi amfani da lokacin hutun nasu wajen tattara bayanai kan ayyukan tare da bayar da rahoto ga majalisar dattijai kan sakamakon bincikensu.

Inda ya ce duk wanda aka samu da hannu wajen tsaikon kammala ayyukan ba zai tafi a banza ba.

Ya ce, “A duk fadin kasar nan, Majalisar Dattawa ta gano cewa akwai ayyuka sama da 10,000 da aka yi watsi da su. Waɗannan ayyuka ne da suka wuce ta hanyar amincewa da kasafin kuɗi kuma an ɗauka cewa an kammala su a cikin takaddun gwamnati.

“Amma lokacin da kuka isa wurin sai ku tarar, babu abin da ake yi. Ina Jami’ar Jihar Osun, da gininta ke Ikire . Na kuma ziyarci Kwalejin Ilimi ta Tarayya, a Iwo.

“A Ikire a nan, akwai kwangilar da aka bayar a 2010 amma ba a kammala ba har yanzu, gidan malamai. Idan ka isa TETfund yanzu, a wajensu, Jami’ar Jihar Osun, da ke Ikire ya kamata a ce tana da gidajen malamai kusan biyar amma daya ne kawai ke aiki a wurin.

“Don haka, mun yanke shawara a Majalisar Dattawa cewa a cikin wadannan shekaru hudu, ba za mu so mu sake ganin irin wadannan ayyukan da aka yi watsi da su ba.

“Sun bukaci dukkan Sanatoci da su koma gida su nemo duk ayyukan da aka yi watsi da su a gundumominmu, mu tattara su. Idan muka koma Majalisar Dattawa, za mu gano dalilin da ya sa aka yi watsi da ayyukan.

“Wanene ke da laifi? Shin ma’aikatar ce? Shin dan kwangilar ne? Shin sun karbi kudin ne suka ki yin aikin? ‘Yan Najeriya za su ji ta bakinmu nan ba da jimawa ba.

“Dole ne wani ya kasance shi ne ke alhakin kuma irin wannan ba zai sami ‘yanci ba. Wadannan na daga cikin gyaran da Majalisar Dattawa ta 10 ke son yi.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet