Labarai
Majalisar Gombe Ta Dakatar Da Tantance Kwamishinoni Saboda Yajin Aikin NLC
Majalisar Dokokin Jihar Gombe a ranar Talatar nan ta dage tantance sunayen kwamishinonin da Gwamna Muhammadu Yahaya ya aika mata.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an tsara fara gudanar da aikin tantancewar ne a ranakun Talata da Laraba, ba tare da la’akari da yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya ta ayyana ba.
Ku tuna cewa gwamnati, Farfesa Ibrahim Njodi, ta aike da jerin sunayen kwamishinoni ga majalisar dokokin a ranar 28 ga watan Yuli.
A cewar wata sanarwar manema labarai da kakakin majalisar Abubakar Luggerewo ya sanya wa hannu, za a tantance sunayen kwamishinoni 17 da suka hada da mata biyu da maza 15 a tsakanin ranakun 7 zuwa 8 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa an dage ne sakamakon yajin aikin.
Yahaya ya mayar da shida daga cikin kwamishinonin sa na farko da wasu sabbin guda 11 cikin jerin wadanda har yanzu ba a tantance su ba.
Ya ce, “Bayan yajin aikin da kungiyoyin kwadagon na hadin gwiwa suke gudanarwa, Majalisar Dokokin jihar Gombe ta dakatar da aikin tantance sunayen kwamishinoni har zuwa ranar Alhamis 7 da Juma’a 8 ga watan Satumbar 2023.”
