Connect with us

Labarai

Kotu Ta Kori Ƙarar Da Sunusi Kiru Ya Shigar Yana Ƙalubalantar Nasarar Kofa

Kotun sauraren kararrakin zaɓe ta tarayya ta Kori karar da Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru na APC ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa na jami’iyyar NNPP.

Kotun ta kori karar ne saboda rashin gabatar da gamsassun hujjojin da za su kalubalaci sahihancin zaɓen ɗan majalisar tarayya a ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji, wanda ya baiwa Abdulmumini Jibrin Kofa na NNPP nasara.

Kotun mai alƙalai Uku ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Ngozi Flora ta bayyana cewa takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya ajiye mukaminsa na babban sakataren hukumar Gidajen tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 sabanin da’awar mai kara.

Ta kuma ce mai shigar da karar ya kasa baiwa kotun hujjojin cewa an tafka kura-kurai a zaɓen ɗan majalisar tarayya na Kiru da Bebeji Inda yace ba’a bi dokar zabe ta 2022 ba a zaben.

“Saboda haka mun kori wannan karar saboda rashin gamsassun hujjoji” a cewar Mai Sharia Ngozi.

Kotun ta kuma umarci wanda yayi kara da ya biya wanda akai Kara Kuɗi naira Miliyan 100,000.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet