Connect with us

Labarai

Adamawa: Akalla Mutane 15 Sun Rasa Ransu Sanadiyyar Kifewar Wani Kwale-kwale

Akalla mutane 15 ne suka nutse a wani tabki bayan da wani kwale-kwale da ke jigilar fasinjoji ciki har da yara ya kife a jihar Adamawa da yammacin ranar Juma’a.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Kwale-kwale da ke dauke da fasinjoji 23 da suka hada da manoma da ‘yan kasuwa da kananan yara daga kauyen Rugange zuwa garin Yola ya kife a tafkin Njuwa da ke kusa da kauyen Dandu a karamar hukumar Yola ta Kudu.

Wani dan agaji na kungiyar agaji ta Red Cross wanda ya zanta da Daily Trust ta wayar tarho daga wurin da lamarin ya faru ya ce an gano gawarwaki hudu.

Majiyar ta ce ma’aikatan jin kai da masu ruwa da tsaki na cikin gida suna cigaba da tsananta neman mutanen da suka bata.

Wani shaidar gani da ido, Faisal Dabo, wanda ya zanta da manema labarai ya ce guguwar iska mai karfi ta sa ruwa ya shiga cikin jirgin wanda kwatsam ya kife.

Ya yi kira ga hukumomi da su samar da jiragen ruwa ga al’ummar Rugange da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa a kogin Benue a duk shekara.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Dakta Muhammad Amin Sulaiman, ya ce an ceto mutane 7, inda aka tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da goma sha biyar kuma ba a gansu ba.

Ya yi kira da a kwantar da hankali yayin da hukumomi ke kokarin gano fasinjojin da suka bata, yana mai cewa za a ci gaba da binciken da karfe 10 na safe ranar Asabar.

Ya bayyana cewa mutane biyu ne suka mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale da ke jigilar mata da maza daga Mayobelwa zuwa Mayo-Ine ranar Litinin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet