Labarai
EFCC Ta Kama Wasu Mutane Masu Damfarar Yanar Gizo Guda 41
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, a ranar Juma’a ta kama wasu mutane 41 da ake zargi da damfarar yanar gizo a garin Warri na jihar Delta.
PUNCH Metro ta tattaro cewa kamen ya biyo bayan wani farmaki da aka kai bisa rahotannin sirri.
An tattaro cewa jami’an shiyyar Benin na hukumar EFCC ne suka kama wadanda ake zargin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ta ce wadanda ake zargin suna da hannu a damfara ta yanar gizo daban-daban, kamar damfara na soyayya, satar shaida, yaudara da kuma karkatar da kudade.
Ta kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun yi maganganu masu amfani kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin, a cewar Uwujaren, sun hada da manyan motoci guda takwas, Toyota Venzas guda biyu, Range Rover daya, Lexus EX 350 daya, Lexus RX 350s guda biyu, Toyota Camry guda daya, Mercedes-Benz C300 daya, Mercedes-Benz GLK, wayoyi da kwamfutar tafi-da-gidanka.
Hukumar ta EFCC ta bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi na masu damfara ta intanet ga ofishin hukumar mafi kusa da su ko kuma ta hanyar yanar gizo.
Hukumar ta kuma jaddada aniyar ta na yaki da cin hanci da rashawa da kuma laifukan tattalin arziki a Najeriya.

Pingback: Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne Sun Kashe Baturen 'Yan Sanda - KAKAKI HAUSA