Labarai
Gwamnatin Kano Za Ta Dawo Da Karbar Harajin Masu Adaidaita Sahu Kullum
Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol yace za’a dawo da karɓar harajin kullum kullum na Masu baburan Adaidaita Sahu.
Digol ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a a helkwatartar Hukumar KAROTA.
Yayin da yake ganawa da Ƙungiyoyin sufurin Adaidai Sahu na jihar nan, ya ce ya zama wajibi Gwamnatin ta ci gaba da karbar harajin ga matuƙa Adaidai Sahu domin ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba.
Kwamishinan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za’a sabunta rijistar Adaidaita Sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu a faɗin jihar Kano
Yace za’a ɓullo da sabbin tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin kullum-kullum tare da sabunta rijistar ba tare da an musguna musu ba, duba da yanayin da ake ci na matsin rayuwa.
KARANTA WANNAN Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Banga Ne Sun Hallaka Baturen Yan Sanda
Ya kuma ce ya zama wajibi Gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa Adaidai Sahun duba da yanayin da ake ciki.
A don haka ko wanne matuƙi dole ne sai ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar nan baki daya.
A nasa jawabin Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir yace sun kula da yadda siyasa ta lalata ɓangaren sufuri a fadin jihar nan, a don haka ba za su zuba ido su bar ɓaraka ta ci gaba da faɗaɗa ba, dole ne a dauki matakin ɗinke ɓarakar.
Shugaban ya ja hankalin ƙungiyoyin Adaidai Sahu su haɗa kansu su zama tsintsiya maɗauri ɗaya domin cin gajiyar tsare-tsaren da gwamnati ke shirin bijiro da su na ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba.
Taron ya samu halartar Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol da shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir da mai bawa Gwamna Shawara a ɓangaren sufuri na jihar Kano Maisalati Garko da kuma kungiyoyin Adaidaita Sahu baki ɗaya.
