Kasuwanci
Ko An Gyara Matatun Mai A Najeriya, Fetur Ba Zai Sauko Ƙasa Da 200 Ba – Dillalai
Kungiyar manyan dillalan man fetur ta Kasa ta ce ba zai yiwu farashin man fetur ya yi kasa da Naira 200 ba, ko da an gyara matatun man.
Kungiyar ta lura da hakan ne biyo bayan wani rahoto da aka buga kwanan nan, inda kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Kasa ta ce farashin man fetur zai fadi kasa da Naira 200 kan kowace lita idan matatun sun fara aiki.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Kasa reshen jihar Ribas Joseph Obele, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar an gyara matatun man kasar kamar yadda aka tsara.
Ya ce, “Har sai matatun man kasarmu sun fara aiki, farashin mai zai daina ci gaba da karuwa saboda sauyin yanayi na kasa da kasa. Amma idan matatun mu suka fara aiki, ‘yan Najeriya za su sayi mai kasa da Naira 200 kan kowace lita.
“Rashin dala ya sa masu shigo da man fetur zai yi dwuya su ci gaba da shigo da shi daga waje. Kimanin makonni biyu ke nan, sarkar rarraba man fetur ta fuskanci tashin hankali. Wannan ya bayyana a kan tashar saye da sayar da mai na NNPC.”
Da yake zantawa da jaridar The PUNCH, babban jami’in gudanarwar kuma tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta Najeriya, Tunji Oyebanji, ya ce canjin dala na shafar farashin man fetur.
Ya kuma ce farashin danyen mai a kasuwannin duniya na hauhawa saboda ragewar da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta yi.
