Connect with us

Labarai

Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 18 Da Aka Sace A Wasu Jihohin Arewa

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Ofusreshin Hadarin Daji a arewa maso yamma da ke karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Najeriya sun ceto sama da mutane 18 da aka yi garkuwa da su a jihohin Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar Ofureshin Hadarin Daji, Captain Yahaya Ibrahim ya fitar a ranar Lahadin nan.

A cewarsa, an samu wannan nasarar ne a lokacin da sojojin da aka tura sansanin ‘Forward Operating Base (FOB)’ da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara suka ceto wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su, bayan wani artabu da ‘yan bindigar a hanyar Anka zuwa Baggega.

Ya ce ‘yan bindigar ne suka yi awon gaba da mutanen lokacin da suka tare hanyar Anka zuwa Baggega tare da yin garkuwa da wasu a cikin wata mota kirar Canter yayin da suke jigilar kayayyaki zuwa kasuwar Baggega da ke karamar hukumar Anka.

Ya kara da cewa sojojin a Zamfara sun ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su daga gonakinsu.

A wani labarin kuma, sojojin da ke aiki da kiraye-kirayen da jama’ar yankin suka yi kan ‘yan bindiga a kauyen Danfanmi da ke cikin garin Kaura, sun yi tattaki zuwa kauyukan wanda ya kai ga ceto mutane uku da abin ya rutsa da su.

“A ranar 8 ga Satumba, 2023, sojojin FOB Baggega a jihar Zamfara, yayin da suke sintiri na yaki, sun tare tare da kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, wadanda suka tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a dajin Gando.

Sanarwar ta kara da cewa, “Bincike na farko ya nuna cewa an yi garkuwa da mutanen ne daga al’ummar Mahuta a jihar Kebbi kuma sun shafe makonni 10 a hannunsu.”

Ya kuma kara da cewa sojojin da aka tura a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun ceto wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su a cikin sa’o’i kadan da ‘yan bindiga suka kai wa garinsu hari.

Kwamandan Rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma Operation Hadarin Daji (OPHD), Manjo Janar Godwin Mutkuta ya yabawa sojojin bisa kwazonsu, juriya da kuma amsa gaggawar kiraye-kirayen da suka kai ga ceto wadanda abin ya shafa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet