Labarai
Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Nemi Sa Hannu FG A Yaki Da Ta’addancin Jihohinsu
Gwamnonin Arewa-maso-Gabas sun koka da yadda matsalar ta’addanci ta ke ci gaba da ta’azzara a yankin a daidai lokacin da ta zargi sarakunan gargajiya da kananan hukumomi a jihohin shida da hada kai da ‘yan bindigar domin haddasa fitina a tsakanin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Gwamnonin a karkashin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da suka fitar a karshen taron su karo na 8 da suka gudanar a Maidugurin jihar Borno a ranar Asabar 9 ga watan Satumba, 2023.
A cikin sanarwar da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai, sun ce taruwar ‘yan bindigar a yankin ya samo asali ne sakamakon hare-haren da sojoji suka kai musu a wasu sassan kasar.
Sun bayyana jihohin Bauchi, Gombe, da Taraba a matsayin mafakar ‘yan ta’adda.
“Yayin da aka amince da nasarar da aka samu a kan ‘yan tada kayar baya, an kara wani sabon salo na ‘yan fashi da makami don ta’azzara matsalar tsaro a yankin. Sakamakon hadin gwiwa da Sojoji ke yi na fatattakar ‘yan ta’adda daga sassan kasar nan, yanzu ‘yan bindigar sun koma yankin Arewa maso Gabas.
“Al’amarin yana kara ta’azzara a Bauchi, Gombe, da Taraba, wuraren da har yanzu ba a kai ga kawar da masu fashi da makami ba. Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sa baki cikin gaggawa don magance wannan matsala.
“Majalisar ta na sane da cewa wasu sarakunan gargajiya da wasu kananan hukumomi suna hada kai da ‘yan bindigar, inda suke ba su mafaka da fakewa don aikata miyagun laifuka a yankin.
“Kungiyar ta yanke shawara daukar mataki don magance duk wani basaraken gargajiya ko shugaban al’umma da aka samu da hannu ko kuma yana hada baki da ‘yan fashi,” in ji shi.
Ya kara da cewa yawaitar hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a yankin na zama matsala, ganin cewa akwai alaka tsakanin ayyukan hakar ma’adinai da rashin tsaro, musamman yadda ake cin zarafin masu hakar ma’adinai.
Don haka taron, ya yi kira ga gwamnatocin da su aiwatar da tanade-tanaden kamar yadda yake kunshe a cikin manufofin hakar ma’adanai na Najeriya tare da jaddada kiran da ta yi na a bi ka’idojin dokar amfani da filaye.
A cewarsu, sauyin yanayi da gurbacewar muhalli wadanda su ne manyan batutuwan da suka shafi yankin na da matukar damuwa.
“Batun ambaliyar ruwa da ta addabi Jihohin da ke haddasa asarar dukiyoyi da asarar rayuka na kara wahalhalun da jama’a ke ciki.
“Hakan ya kara hanwo tabarbarewa sakamakon yadda kogunanmu ke yi da kuma sare itatuwa da sana’ar gawayi ke haifarwa. Akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani a fannin kawar da koguna.
“Bugu da ƙari kuma, akwai buƙatar gudanar da ingantaccen sarrafa sare dazuzzuka tare da ƙaƙƙarfan ƙa’ida ga hukumomin gida kan rashin amincewa da ba da izini ga irin wannan kasuwancin.
“Taron ya yanke shawarar yin la’akari da shirin Duniya na Carbon Credi, Babban Ganuwar Koren, da sauran tsare-tsare da za su dakile mummunan tasirin sauyin yanayi a yankin, “in ji shi.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnonin Adamawa, Bauchi, Borno, da Yobe; yayin da gwamnonin Gombe da Taraba suka samu wakilcin mataimakansu.
