Labarai
Adamawa: An Cafke Wasu Matasa Bisa Zargin Su Da Laifin Fashi Da Makami
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da laifin aika fashi da makami a Yola babban birnin jihar.
“ A Wasu dabarun aiki da kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, CP Afolabi Babatola, ya bullo da shi, don kawar da ayyukan ‘yan ta’addanci a cikin babban birnin jihar, ya haifar da sakamako mai kyau yayin da aka kama wasu ɓarayi guda hudu,” in ji rundunar ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da jama’a, SP Suleiman Nguroje.
Sanarwar ta nuna cewa wadanda ake zargin masu shekaru 18 zuwa 23 ne, sun yi wa wasu mazauna unguwannin Demsawo da Nasarawo da ke Jimeta, a karamar hukumar Yola ta Arewa fashi.
Wadanda ake zargin sun hada da Kabiru Yahaya mai shekaru 18, kuma mazaunin titin Kala’a; Abdulazeez Mohammed mai shekaru 23 kuma mazaunin Wuro Kuturu; Adamu Babayo mai shekaru 18 kuma mazaunin titin Bauchi; da Ibrahim Mohammed mai shekaru 20 kuma mazaunin Nasarawo Borehole, duk a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa.
An kama su ne a ranar Lahadi, 10 ga Satumba, tare da hadin gwiwar tawagar ‘yan sanda da mambobin kungiyar Tallafawa Tsaron cikin gida (’yan banga).
An kwato muggan makamai da babur dinsu na aiki daga hannunsu.
Nguroje ya bayar da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya kamar yadda doka ta tanada.
