Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire Biyu A Jihar

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bayar da umarnin dakatar da shugabannin sakandiren koyon harshen Faransanci da na Sakandiren koyon harsunan kasar Sin, da ke Kwankwaso a ke karamar hukumar Madobi a jihar nan take saboda rashin zuwa aiki da kuma sakacin rashin baiwa dalibai abinci.

Hakazalika, ma’aikatar ta amince da nada Umar Akilu Sabo a matsayin shugaban riko na makarantar Sakandiren koyon harshen Faransanci da kuma Isyaku Umar Abdullahi a matsayin shugaban sakandiren koyon harshen kasar Sin da ke Kwankwaso.

Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar a ranar Litinin din nan, ta ce shugabannin da aka dakatar ba sa cikin makarantun a lokacin da tawagar jami’an gwamnati suka kai ziyarar gani da ido a ranar Litinin domin sanya ido kan yadda za a fara karatun zangon farko na shekarar 2023/2024.

Sanarwar ta ce, tawagar da ta sa ido a karkashin babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Kubra Imam, ta gano cewa ba a ba wa daliban kwalejojin biyu abinci a daren ranar Lahadi ba, kuma ba a shirya musu buda baki da za su ci a safiyar ranar Litinin ba har zuwa lokacin ziyarar.

Kwamishinan ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya kira halin rashin kulawa da shugabannin biyu suka nuna, don haka ya umarce su da su mika al’amuran makarantar ga sabbin shugabannin makarantar su kuma kai rahoto ga ma’aikatar har sai an gudanar da bincike.

Doguwa ya gargadi daukacin shugabanni makarantu da su yi watsi da duk wani abu da zai kawo cikas ga kokarin gwamnati mai ci na farfado da fannin ilimi.

A halin da ake ciki, kwamishinan ya yabawa shugabar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke Kofar Famfo da takwararta ta makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamanti da ke Kwankwaso bisa jajircewa da kuma bijirewa duk shirye-shiryen da ake bukata domin fara karatun zangon farko na shekarar 2023/2024.

“Dalibai sun gamsu da yadda ake ba su abinci. Fitowarsu abin yabawa ne matuka, kuma Shugabannin Makarantun biyu sun yi namijin kokari wajen ganin an kyautata muhallin makarantunsu,” kamar yadda kwamishinan ya bayyana a cikin sanarwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet